​Yemen: An Kai Hari A Kan Sansanin Sojojin Hayar Saudiyya A Garin Ma’arib

2020-05-21 16:35:52

Rahotanni daga Yemen na cewa, sojoji da dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar sun kai harin ramuwar gayya ta hanyar harba makami mai linzami a kan sansanin sojojin hayar Saudiyya da ke garin Ma’arib na kasar ta Yemen, kuma an ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi a wurin.

Tashar Almasirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, bayan harin da dakarun kasar ta Yemen suka kai a garin Qaniya da ke karkashin ikon sojojin hayar Saudiyya, wannan ya ba su damar nausawa zuwa garin na Baida dake tsakiryar kasar, wanda yana daga cikin yankuna masu arzikin man fetur na kasar ta Yemen da Saudiyya ta mamaye.

A cikin ‘yan makwannin da suka gabata, duk da ikirarin da sojojin kawancen Saudiyya suka yi na dakatar da bude wuta, amma sun ci gaba da kai hare hare ta sama da kasa a sassa daban-daban na kasar ta Yemen a cikin wanannwata na Ramadan mai alfarma, wanda hakan yasa dakarun kasar na Yemen suka sha alwashin mayar da martani mai tsanani kan hakan.


Tags:
Comments(0)