​Najeriya: Mataimakin Shugaban Kasa Ya Killace Kansa

2020-03-25 13:58:09

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya killace kansa na kwanaki 14 kamar yadda hukumar NCDC ta shawarce shi.

A cikin rahoton da jaridar Primum Times ta bayar ta bayyana cewa, Kakakin sa Laolu Akande ya sanar a shafin sa ta tiwita cewa, Farfesa Osinbajo na aiki a dakinsa shi kadai ba tare da wani ya ziyarce shi ba.

Ba a fadi ko da wa ya yi mu’amala ba, sai dai bayanai sun nuna cewa, mai yiwuwa ya yi hakan ne saboda cudanya da ya yi da wasu manyan jami’an gwamnati a cikin ‘yan kwanakin nan, wadana kuma aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari na daga cikin manyan jami’an gwamati da aka tabbatar da cewa suna dauke da cutar.

Sannan kuma sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi wa gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed na coronavirus, ya nuna cewa gwamnan na dauke da cutar.

Yanzu dai gwamna Bala ya killace kansa ,sannan likitocinsa sun isa wurinsa tare da jami’an hukumar NCDC.

Tags:
Comments(0)