​Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Hanyoyin Yin Aiki Tare Wajen Yaki Da Corona

2020-03-25 13:57:08

Ministocin harkokin wajen kasar Iran da Rasha sun tattauna kan hanyoyin da za su bi wajen karfafa yin aiki tare, domin yaki da yaduwar cutar corona.

A zantawar da suka yi ta wayar tarho a yau Laraba, ministocin harkokin wajen kasashen Iran Muhammad Jawad Zarif, da kuma na Rasha Sergey Lavrov, sun tattauna kan irin illar da cutar corona take ci gaba da yi a duniya, da wajabcin daukar matakai na hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya domin murkushe wannan cuta.

A yayin zantawar, ministocin harkokin wajen kasashen na Iran da Rasha, sun cimma matsaya kan gudanar da wasu ayyuka na musamman tsakanin kasashen biyu, domin dakile yaduwar cutar ta corona a cikin kasar Iran.

A daya bangaren kuma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi kakkausar a kan gwamnatin kasar Amurka, dangane da ci gaba da kakaba takunkumin da take yi a kan Iran a cikin wannan hali, inda ya ce matakin ya yi hannun riga da ‘yan adamtaka.

Ya ce Rasha za ta ci gaba da bin dukkanin hanyoyin da suka dace a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da sauran hanyoyi, domin ganin duniya ta matsa lamba kan Amurka, domin ta janye takunkuman da ta kakaba wa Iran, wadanda suke kawo cikas a yakin da ake yi da corona.

Tags:
Comments(0)