​Ministan Tsaro Kasar Sudan Ya Rasu

2020-03-25 13:17:06

Rahotanni daga kasar Sudan sun Ambato cewa, ministan tsaron kasar Jamaluddin Umar ya rasu a yayin wata ziyarar aiki da yake kai wa a kasar Sudan ta kudu.

Jaridar Shar Al-ausat ta bayar da rahoton cewa, Laftanar Janar Jamaluddin Umar yana halartar wani taron tattaunawar sulhu tare da ‘yan tawayen Sudan a birnin Juba na Sudan ta kudu.

Rahoton ya ce, Umar ya rasu ne sakamakon tsayawar zuciyarsa daga aiki, kuma a halin yanzu haka na birnin na Juba ana gudanar da shirye-shiryen dauko gawarsa zuwa birnin Khartum.

Jamaluddin dai ya kasance tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Sudan a lokacin mulkin Umar Hassan Albashir, amma bayan hambarar da Albashir, Abdulfattah Burhan ya sanya a matsayin daya daga cikin mammbobin majalisar mulki ta kasar, daga bisani kuma ya ba mukamin ministan tsaro na kasar ta Sudan.

Tags:
Comments(0)